Loading....

JAMB UTME - Hausa - 2011

Question 1 Report

HARSHE: AUNA FAHIMTA

A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kammala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare. Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.

Bayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.

Da ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.

Ganin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun. Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’

Mece ce dangantakar Salihi da Ɗahira?