HARSHE: AUNA FAHIMTA A karanta wa?annan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu. Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayu...

Question 1 Report

HARSHE: AUNA FAHIMTA

A karanta wa?annan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin biyu: ?aya ya yiwu an ci an ?oshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.

Kullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.

A al?adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ?osai ko kunu. Wasu kuma, sukan ?umama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ?anwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko ku?ewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai ?Daidai ruwa daidai ?urji.?

Har ila yau, ko da yake ba kowa yake da ?arfin ?ora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami ma?wabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira ma?wabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ?an?uwansa.

A zamanin da, za a ga Bahaushe yana ?o?arin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.

Me ake nufi da gwama nunfashi a labarin?